Buhari ya sake sabunta nadin jakadu 12, duba sunayensu - Garba Shehu


Biyo bayan nadin sabbin kananan jakadu 41, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma amince da sabunta nadin wasu tsoffin jakadu 12. Sabunta mukamin nasu ya biyo bayan bita da nazari a kan kwazon aiki da suka yi a baya, wanda bukata ta sanya shugaban kasar ya amince da su ci gaba rike kujerunsu a matsayin jakadu.

Jerin jakadu 12 da kuma jihohinsu wanda aka sabunta nadinsu kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito sun hadar da;

Mrs Uzoma E. Emenike (Abia); Yusuf M. Tuggar (Bauchi); Muhammad B. Madugu (Bauchi); Ambasada Baba Ahmad Jidda (Borno); Uyigue O. Oghogho (Edo); Dr Eniola Ajayi (Ekiti); Deborah S. Iliya (Kaduna); Mohammed D. Rimi (Katsina); Farfesa Tijjani Muhammad-Bande (Kebbi); Dakta Modupe E. Irele (Lagos); Adeyinka Asekun (Ogun); da Sanata Goni Modu Zanna Bura (Yobe) Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun sa, Garba Shehu, ya ba ‘yan Najeriya tabbacin yin adalci yayin nadin wakilci da kuma dukkan abin da ya shafi shugabanci.

Shugaban kasar ya ba da tabbacin hakan ne biyo bayan korafin da aka yi kwanan nan bayan nadin sabbin jakadu 41 da ya yi, inda wasu jihohin kasar suka tashi fayau. Shugaba Buhari, wanda ya sake taya jakadun murna sabunta mukaminsu, ya bukaci da su ci gaba da rike martaba da kuma inganta dabi'un shugabanci a Najeriya, yayin da suke rike kyakkyawar alaka da sauran kasashe.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, shugaba Buhari ya ayyana sunayen mutum 41 da zai nada a matsayin kananan jakadun Najeriya zuwa kashen ketare Hakan na kunshe ne a wasikar da shugaba Buhari ya aike wa majalisar dattawa na neman amincewarta da mutanen da za su wakilci Najeriya a wasu kasashe na ketare.

Shugaban Majisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, shi ne ya bayyana hakan yayin karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba. Wannan sabuwar bukata da shugaban kasar ya shigar ta biyo bayan amincewar majalisar da sunayen wasu mutum 42 da shugaban ya nada manyan jakadu a watan Mayu.

Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN