Cire cikin shege tare da binne jariri da ransa: Yansanda sun kama Hauwa da Zainab a Kaduna

Rundunar yansandan jihar Kaduna ta kama wata mata mai suna Hauwa mai shekara 33 bisa zargin hada baki da yayarta Zainab mai shekara 35 suka cire cikin da take dauke da shi a birnin Kaduna ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na safe a unguwar Tudun wada.

Rahotannin farko sun bayyana cewa matan guda biyu sun aiwatar da wannan danyen aiki ne bayan sun biya N2000 kudin dakin wani Otel mai suna People's Club Hotel ranar Juma'a suka shiga domin su kwana. Amma sai suka yi amfani da wannan lokaci suka cire cikin da Zainab take dauke da shi.

Bayanai sun nuna cewa ba mamaki tsananin matsi daga gidansu ne ya sa Zainab ta yanke shawaran zubar da cikin.

Hakazalika bayanai sun nuna cewa wani bawan Allah ne ya gan yan matan suna gina rami da ice, a harabar wannan Ootel, bayan sun bar wurin sai ya kira wani mutum suka je suka duba abin da aka binne.

Daga bisani suka ga jini yayin da suke cikin tone wajen, sai suka je suka shaida wa yansanda da suka zo suka tone wajen kuma suka tarar cewa jariri ne aka binne, kuma ya mutu.

Tuni yansanda suka kama tare da buga wa yan matan ankwa, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN