Cikakken rahotun ababen da suka faru da Ibrahim Magu ranar Juma'a

Rahotun Legit Hausa

Zargin rufa-rufa: 'Yan daba sun kutsa ofishin NFIU, sun ragargaza kwamfutoci

Akwai wani abu mai kama da rufa-rufa a hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ke faruwa. Akwai yuwuwar hakan na da alaka da binciken dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu da ake yi tun daga ranar Litinin.

Wasu 'yan daba ne suka balle ofishin sashen sirrin kudi na Najeriya (NFIU) inda suka ragargaza na'urori masu kwakwalwa da ke dauke da bayanai da takardu masu matukar amfani ga binciken. Jaridar THISDAY ta gano cewa, wannan ci gaban ne yasa wasu jami'an NFIU suka bayyana gaban kwamitin bincike na Mai shari'a Ayo Salami, inda ake bincikar Magu.

An kira su ne don karin haske game da wasu takardun da suka jibanci wasu kudi da aka zarga an fitar. Amma kuma jami'an NFIU sun sanar da kwamitin cewa a ka'idar aikinsu, basu yawo da takardu. Jami'an sun shawarci kwamitin da su samesu a ofishinsu a ranar Juma'a da safe don ganin takardun da suke bukata.

Sai dai kuma, kafin isar mambobin kwamitin ofishin a safiyar Juma'a, wasu mutane da ba a sani ba sun balle ofishin inda suka isa kai tsaye dakin da ake adana bayanan a kwamfuyuta suka ragargazasu. Bayan aukuwar hakan, jaridar THISDAY ta gano cewa, darakta janar na NFIU, Modibbo Hamman-Tukur, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan rahoton aukuwar lamarin.

Wata majiyar ta ce hakan ce ta sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu. A halin yanzu, balle ofishin NFIU shine rufa-rufa babba a kan bincikar Magu da ake yi kuma ana bincike a kan hakan.

A wani labari na daban, wasu daraktocin hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da wasu manyan jami'an hukumar, a ranar Alhamis sun bayyana gaban kwamitin bincike. Kwamitin binciken ya samu jagorancin Mai shari'a Ayo Salami a kan zargin rashawa da ake wa dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Daga cikin wadanda suka bayyana gaban kwamitin akwai sakataren EFCC, Olanipekun Olukoyede. Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an bincikesu na fiye da sa'o'i 12. An gayyacesu ne don su bada abinda suka sani game da wasu zargi da ake wa Magu.


Da duminsa: An janye dogaran Ibrahim Magu gaba daya, an canja musu wajen aiki


Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa hukumar yan sandan Najeriya karkashin jagorancin IGP Mohammed Adamu, ta janye dogaran mukaddashin shugaban hukumar EFCC da aka dakatar Ibrahim Magu gaba daya. Tashar TVC ta bayyana cewa tuni an canza musu wuraren aiki kaman sauran jami'an yan sanda.

Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Magu - Ministan shari'a



A yau, Juma'a, ne ministan shari'a sannan babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da Ibrahin Magu, mukaddashin shugaban EFCC.

A cikin wani jawabi da kakakinsa, Umar Gwandu, ya fitar, Malami ya ce shugaba Buhari ya dakatar da Magu ne domin bawa kwamitin binciken da aka kama damar yin aikinsu ba tare da wani katsalandan ba. "Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin darektan gudanarwa a hukumar EFFC, Mohammed Umar, a matsayin shugaban riko na hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a kammala bincike da sanar da mataki na gaba," a cewar sanarwar.

Legit.ng ta wallafa cewa jam'iyyar PDP ta bukaci a gurfanar da Magu bayan dakatar da shi domin tuhumarsa da aikata almundahana. PDP ta bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da sakatarenta na watsa labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, a Abuja.

A cewar PDP, ta bukaci a gurfanar da Magu ne bayan nazarin dalilan da su ka sa har shugaban kasa ya kafa kwamitin bincike a kansa. Jam'iyyar ta bayyana cewa binciken da ake gudanarwa a kan Magu ya tabbatar da zargin da ta dade ta na yi a kan cewa hukumar EFCC ta na rufawa jami'an gwamnati mai ci aisri tare da tozarta mambobin jam'iyyun adawa.

A cewar Ologbondiyan; "bankado yadda Magu ya dinga sayar da kadarorin da EFCC ta kwace kamar yadda ministan Shari'a ya bayyana a cikin takardar korafi da kuma rahoton da ofishin hukumar DSS ya fitar, sun tona asirin irin cin mutunci da gwamnatin jam'iyyar APC ta yi wa wasu 'yan Najeriya da sunan yaki da cin hanci."

Abubuwan da su ka fito fili yanzu sun kara haskaka dalilan da suka sa yaki da cin hanci ya kara tabarbarewa a karkashin mulkin Buhari, kamar yadda sahihan kungiyoyin kasa da kasa suka nuna a cikin rahotanninsu. "Ba kankanin abin kunya bane ga Najeriya a samu shugaban hukumar yaki da cin hanci da laifin aikata almundahana tare da barnatar da dukiyar da aka kwace domin mayarwa hannun gwamnati. "

Tunda yanzu asirinsa ya tonu, bai kamata shugaba Buhari ya ke kokarin nemawa Magu sassauci ko hana a gurfanar da shi a gaban kotu ba," in ji Ologbondiyan. Magu, wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da shi, ya na fuskantar tuhume - tuhume ma su nasaba da almundahana da kama karya da sharara karya a gudanar da aikinsa na yaki da cin hanci da rashawa. A ranar Litinin ne Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin bincikensa da aka kafa a fadar shugaban kasa.

Magu ya nemi beli a wurin IGP



Dakatattacen mukadashin shugaban yaki da rashawa ta EFCC, Mr Ibrahim Magu da ake bincika a kan zargin rashawa ya nemi Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar da shi beli.

Kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa karkashin jagorancin tsohon alkalin kotun koli Ayo Salami ne ke bincikar Magu. Magu, wanda aka tsare tun ranar Litinin ya rubuta wasika ta hannun lauyansa, Mr Oluwatsosin Ojaomo a ranar Juma'a zuwa ga IG na neman beli kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Tun ranar da aka kama shi, Magu yana tsare ne a wani wurin ajiya na rundunar 'yan sanda a Abuja inda daga nan ya ke zuwa gurfana gaban kwamitin binciken. Wasikar da lauyansa ya rubuta zuwa ga ofishin IGP mai dauke da kwanan wata na 10 ga watan Yuli kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ta nemi a bayar da shi beli, "bisa sanayar da aka masa a kasa."



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN