• Labaran yau


  Duba dalili da ke sa ake samun Ƙagewar hannu bayan karaya

  Physio Hausa

  Daga cikin matsalolin da ke nakasa hannu bayan raunuka akwai matsalar nan da ake ce mata "volkman's ischemic contracture" a turancin likita. Wannan matsala ce da ke faruwa yayin da aka sami rauni a dantsen sama ko na ƙasa, kamar karaya, ƙunan wuta, da sauran raunuka.


  Sakamakon wannan lahani, za a sami gajercewar tsokokin dantsen ƙasa, kuma gajercewar tsokokin zai haifar da kassarewar ayyukan tsintsiyar hannu, tafin hannu da yatsu, hakan zai sa gaɓoɓin tsintsiyar hannu, tafin hannu, da yatsu su ƙage.


  Da zarar an lura hannu ya ƙage bayan karaya, ƙunan wuta ko wani rauni a dantsen sama ko ƙasa, a tuntuɓi likitan fisiyo kafin matsalar ta kai ga yin aiki/tiyata don sakin jijiyoyin hannun.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba dalili da ke sa ake samun Ƙagewar hannu bayan karaya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama