An kama matasa 2 da suka yiwa wata yarinya fyade suka kuma kashe ta a jihar Naija

Jami’an ‘yansandan jihar Naija sun kama wasu matasa 2 da zargin kashe wata matashiya ‘yar shekaru 18 bayan sun mata fyade.

An kama Abdulkadir Alhaji Ibrahim me shekaru 25 da kuma Abubakar Idris me shekaru 29 a kauyen Fulani na Doko dake, karamar hukumar Lavun, jihar Naija bayan sun ja yarinyar zuwa daji inda suka mata fyade sannan suka daddatsa ta da wuka, kamar yanda me magana da yawun ‘yansandan jihar, ASP Wasiu Abiodun ya tabbatar.

Yace wanda ake zargi sun amsa laifinsu kuma da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu gaban kotu.

hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post