Wata mata mai ciki me suna Jane Ekpe, mai shekara 32, an
ruwaito mutuwarta ta hannun wani Florence Ugwu, mai shekara 34, a
kasuwar Okwo Ngbo da ke karamar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi.
Marigayiyan, wanda aka ce tana cikin kusan wata shida, ta mutu a asibiti inda aka garzaya da ita bayan fadan a Ugwu.
An tattara matan biyu sun yi cacar baki a kasuwar Okwu a
ranar 11 ga Yuli, lokacin da Ugwu ta shure marigayiyar a ciki sai ta
fara zubda jini.
An garzaya da ita asibiti inda ta haifi bakwaini kafin ta mutu.
Kakakin ‘yan sanda, Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce Kwamishinan ‘yan sanda, Philip Sule Maku ya ba da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin.
“DPO ya hanzarta tattara mutanensa zuwa wurin sannan suka dakko gawar sannan aka ajiye at a babban asibitin garin Ngbo”
“Nan da nan aka kama wadda ake zargi kuma aka tsare ta a
ofishin su, kuma bincikensu na ci gaba da gudana amma batun ya wuce
karfin su.”
hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/