• Labaran yau


  Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Katsina, akalla shida sun mutu

  Wasu bama-bamai da sun tashi a kauyen Yammama, a karamar hukumar Malumfashi ya jihar Katsina kuma mutane da dama sun rasa rayukansu.

  Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne da safiya Asabar a gonar wani mutum mai suna Alhaji Hussaini Mai Kwai.

  Har yanzu ba'a san ainihin adadin wadanda suka rasa rayukansu amma masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akalla mutane shida sun mutu.

  Wani mai idon shiada yace wadanda suka mutu leburori ne dake cire ciyayi a gonar. "Na kirga gawawwaki 6 kuma an garzaya da wasu 5 asibiti. Jami'an tsaro sun killace wajen yanzu." Majiyar ta ce. Saurari karin bayani....

  Source: Legit


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Katsina, akalla shida sun mutu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama