Kwamishinan Ilimi na jihar Sanusi Muhammad Kiru ya sanar wa Manema labarai haka ranar Alhamis a lokacikin wani taro da manema labarai.
Ya ce an killace akalla mutum 1860 a Cibiyoyi guda uku da aka tanada don killace masu cutar a fadin jihar, wanda aka sami mutum 193 dauke da cutar a cikin adadin mutanen da aka killace.
Sanusi, wanda shi ne babban jami'in Gwamnatin jihar Kano da ke kula da lamarin Almajirai a jihar, ya ce Almajirai 86 sun kamu da cutar a gwajin da aka yi a wajen killacewa na Gabasawa, 68 a wajen killacewa na Karaye sai kuma 38 a Kiru.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari