Wani matashi dan kimanin shekaru 25 a karamar hukumar Tafawa Balewa dake
jihar Bauchi ya yiwa wata yarinya me shekaru 7 kacal da haihuwa inda ya
barta a Asibiti tana fama da rayuwarta.
Hajiya Zainab Babba-Tanko me
gidauniyar Babba Takko ce ta bayyanawa manema labarai haka a Ranat
Alhamis inda tace matashin da ya ranta a Nakare ya ajiye yarinyar ne
kusa da Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa bayan ya mata
fyaden.
Me magana da yawun ‘yansandan Jihar, DSP Wakili ya bayyana cewa, bai samu wannan Rahoto ba tukuna.Abubakar
Sani me kimanin shekaru 28 na kauyen Nasarawa dake karamar hukumar Gumi
a jihar zamfara ma an kamashi da zargin yiwa yarinya me shekaru 4
fyade.
Hukumar jami’an tsaro na Civil Defence ne suka kamashi ranar 30 ga
watan Yuli inda aka kaishi Gusau dan daukar matakin daya kamata.Hakanan
babbar Kotun dake Bompai, Kano ta yankewa Abdullahi Magaji na karamar
hukumar Kumbotso hukuncin shekaru 14 a gida yari bayan samunshi da
laifin yiwa ‘yar shekaru 6 fyade a shekarar 2016.Kotun ta kuma bukaci me laifin daya biya diyyar Dubu dari 200 ga wanda yawa aika-aikar, sannan
Wata Dubu dari 200 ga kotun.Hakanan
hukumar ‘yansandan jihar Kanon ta gurfanar da mutuminnan, Muhammed Alfa
da ake zargi da yiwa mata 40 fyade da kuma wata tsohuwa ‘yar shekaru
85, an gurfanar da wanda ake zargi a kotun Nomansland dake Sabon gari.Hakanan
a jihar a garin abakaliki na Jihar Ebonyi wata kotu ma ta daure wani
mutum me shekaru 42 da aka samu da laifin yiwa ‘yar shekaru 14 fyade.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari