Jami’an ‘yansanda sun kama wani Sha’aibu Aliyu a garin Kalambaina dake
karamar Hukumar Wammako dake jihar Sakkwato da zargin yiwa wata yarinya
da ba’a bayyana sunan ta ba me shekaru 14 fyade wanda kuma har ta
haihu.
Bayan haihuwartane sai ta kai masa jaririyar amma sai shi da wani
abokinsa, Nasiru Attahiru suka je suka jefar da ita a jeji.
Saidai Allah
ya taimaka wasu suka ga Jaririyar suka kaiwa mahukuntan karamar hukumar
Wammako wanda su kuma suka kaiwa ‘yansanda kara.
Kwamishinan ‘yansandan
jihar, CP Sani Kaoje ya tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce abokin
Shu’aibu da suka yi aika-aikar tare ya tsere amma suna kan nemanshi.
Yace
akwai kuma wani mutum shima, Ahmad Alhaji Dahiru Maibuhu da yawa wata
yarinya me shekaru 12 fyade wanda an kamashi. Lamarin ya farune a
Rumbukawa dake Illela.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari