Yan Acaba ko Okada a birnin Lagos sun gudanar da zanga zanga sakamakon zargin cewa wani dansanda ya kashe daya daga cikin yan Acaba ranar Alhamis da dare.
Bayanai da muka samu sun nuna cewa yan Acaban sun aikata barna ga dukiyan bayin Allah da tsakar raanar Juma'a a Ojo, yayin da yansanda suka ja daga suna harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Majiyarmu ta ce lamarin na neman kazancewa, amma duk da kasancewar Barikin Soji na Ojo na ketaren titi ne daga inda lamarin ke faruwa, babu wani abin da suka yi domin koran masu zanga zangan a wajen.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari