• Labaran yau


  Kashe DPO da yansanda 7 a jihar Kogi, duba matakin gaggawa da IGP ya dauka kan yan fashi

  Yansanda 8 tare da farar hula 1 sun mutu a garin Isunlu a jihar Kogi ranar Alhamis bayan wasu miyagun yan fashi da makami sun farmaki garin.

  DPO na yansanda na cikin yansanda da yan fashin suka halaka bayan sun kai hari a ofishin yansandan, suka saki wadanda aka tsare, daga bisani suka harbe yansandan har lahira.

  Rahotanni sun ce bayan yan fashin sun halaka yansandan, sai suka zarce zuwa wani Banki suka kwashi kudi da ba a san adadinsu ba.

  Sakamakon haka shugaban yansandan Najeriya Muhammed Adamu ya bayar da umarnin kaddamar da gagarumin bincike domin kama yan fashin da suka yi wannan aika aika.

  Hukumar yansandan Najeriya ta fitar da wannan sanarwa a shafinta na Twitter, cewa shugaban yansanda Muhammed Adamu ya abayar da umarnin yin binciken kwakwaf kan lamarin.

  Tuni Shalkwatan yansandan Najeriya ta aika kwararrun jami'anta na sashen Intelligence Response Team (IRT), da Special Tactical Squad (STS) da Federal-SARS suna cikin wadanda IGP ya tura jihar Kogi domin su binciko, kuma su kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki ga jami'an yansanda.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kashe DPO da yansanda 7 a jihar Kogi, duba matakin gaggawa da IGP ya dauka kan yan fashi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama