Zargin banbanci wajen raba mukamai: Yan kudu sun kai Buhari Kotu don neman diyyar N50b

Wasu gamayyar ‘yan kudu sun kai shugaban kasa,Muhammadu Buhari kara wajan babbar kotun gwamnatin tarayya bisa jagorancin mayan lauyoyi masu mukamin (SAN) 10 inda suke bukatar ta bi musu hakkinsu saboda zargin gwamnatin shugaban kasar da nuna banbanci wajan nade-naden mukamai.

Sun zargi cewa wannan nuna banbanci ya yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya karan tsaye wanda ya bukaci raba daidai wajan mukamai a kasarnan.

Sun kuma zargi cewa bashin da gwamnati ta ciwo na Dala Biliyan 22.7 yawanci Arewa ce za’a wa aiki dashi inda aka baiwa kudu kaso kadan.

Sun kuma bukaci kotun data hana shugaban kasar ciwo bashi nan gaba wanda zai sha kan Najeriya. Wanda suka kai wannan kara sun hada da Chief Edwin Clark, Chief Reuben Fasoranti, da dai sauransu

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN