Yanzu yanzu: Wani jirgin sama mai saukar angulu ya fado da Kwamishinan yansanda - Hotuna

Wani karamin jirgin sama na yansandan kasar Kenya ya fado ranar Asabar 13 ga watan Yuni a gabacin Meru yayin da yake kan hanyasa ta zuwa  Marsabit dauke da jami'an yansanda

Mun samo cewa Kwamishinan yansanda na yankin gabacin yankin tare da wasu jami'ansa na kan hanyarsa ce ta zuwa taro da takwaransa na yankin arewaci kafin faruwar lamarin.

Kakakin yansandan kasar Kenya Charles Owino, ya ce Jirgin mai saukar Angulu yana dauke da mutum shida, biyu matuka jirgin ne, mutum hudu kuma jami'an yansanda.

An kwantar da wadanda suka sami raunuka a Asibitin Meru Level 5 inda suke samun kulawan Likitoci.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post