• Labaran yau


  Dokar hana zirga zirga: Matashi ya kara nauyi p224 saboda zama a gida har wata biyar

  Wani matashi mai suna Mr Zhou dan shekara 26 a birnin Wuhan na kasar China ya kara nauyi har pounds 224 sakamakon rashin fita har tsawon wata  biyars saboda dokar hana zirga zirga kan cutar Korona

  Mr Zhou  ya daina zuwa wajen aiki ne a Internet Caffe, wanda yake motsa jiki ta hanyar takawa da kafa zuwa wajen aiki, ya kamu da rashin lafiya sakamakon kara nauyi da ya yi a cikin yan watanni.

  Yan uwaansa sun ce yana fama da matsalar motsa jikinsa bayan ya kara matukar nauyi.

  Wasu hotuna da Asibitin Zhongnan na Jami'ar Wuhan ta fitar, sun nuna yadda Likitoci suke faman kulawa da Mr Zhou lokacin da aka shigo da shi da gaggawa.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dokar hana zirga zirga: Matashi ya kara nauyi p224 saboda zama a gida har wata biyar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama