• Labaran yau


  Yan fashi sun kashe wata daliba bayan sun yi mata fyade

  An kashe wata dalibar kwaleji da aka sassara da adda bayan an yi mata fyade a cikin coci.

  Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce Grace Oshiagwu ta rasu ne bayan matsfan sun yi mata fyade sun kuma sassare ta.

  Aminiya ta ruwaito cewa aika-aikan na zuwa ne kimanin makonni biyu da aka yi wa wata budurwa mai suna Barakat Bello fyade aka aka kuma kashe ta a yankin.

  A karamar Hukumar ta Akinyele ce kuma aka yi wa wata mata mai juna biyu da ke karatu a jami’a fyade aka kuma kashe ta.

  Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo Olugbenga Fadeyi, ya kara da cewa, “Mun fara gudanar da bincike da kokarin gano miyagun domin a hukunta su.

  “Muna rokon duk mai wani kwakkaran bayani da ya taimaka domin mu magance wannan danyen aiki”, inji shi

  Rahotun Aminiya

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan fashi sun kashe wata daliba bayan sun yi mata fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama