Kasar Saudiyya na duba yiwuwar dakatar da gudanar da aikin Hajjin bana saboda yaduwar cutar COVID-19 a kasashen duniya.
Tuni dai Gwamnatin Saudiyya ta umarci manyan malaman kasar da su yi nazarin lamarin su ba ta fatawa.
A karon farko ke nan za a yi fashin aikin Hajji a sama da shekaru 100 saboda annaobar, muddin ba yi ba a bana.
Ministan Ayyukan Hajji da Umara Saleh bin Taher Banten ya shaida wa gidan talbijin na kasar cewa mahukuntan kasar na ba da muhimmanci matuka ga rayuka da lafiyar mahajjata
Don haka ya shawarci maniyyata aikin Hajji a bana da su jinkirta har zuwa lokacin da kasarsa za ta fitar da matsaya.
“Mahukuntan Saudiyya a shirye suke su kare lafiyar Musulmi a fadin duniya, don haka muke kira ga maniyyata su dakata har sai an fitar da matsaya”, inji ministan.
Saleh bin Taher Banten yana daga cikin manyan masu ba da shawara kan al’amuran aikin Hajji da Umara na duniya wanda yake da ra’ayin jinkirta har sai an kai lokacin da za a iya fahimtar tasirin annobar Coronavirus.
Rahotun Aminiya
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari