Sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa manema labarai ranar Lahadi ta tabatar da rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar cewa an yi rikici a fadar sakamakon hatsaniya da ta barke tsakanin mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari da da wani mai taimakawa shugaban kasar Sabi'u Yusuf.
Jaridun Najeriya sun ambato wasu majiyoyi da ke cewa lamarin ya faru ne bayan Sabi'u Yusuf, wanda aka fi sani da 'Tunde' ya koma fadar ta shugaban kasa bayan balaguron da ya yi zuwa Lagos, inda kuma bai killace kansa tsawon kwana 14 ba kamar yadda dokokin hukumar yaki da cutuka masu yaduwa suka gindaya.
Rahotannin sun ce Aisha Buhari ta bayyana masa rashin jin dadinta a gare shi lamarin da ya kai ga ce-ce-ku-ce a tsakaninsu, kuma dalilin hakan ne masu tsaron lafiyarta suka yi harbe-harbe a sama.
Hakan ya saba wa doka, kamar yadda sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana ko da yake bata fito karara ta yi bayani kan ko hatsaniyar da ta faru ba.
"Wannan lamari ya faru ne a wajen gidan shugaban kasa. An bai wa jami'an da ke dauke da makamai da na tsaro horo musamman kan yadda za su sarrafa makamai kuma idan suka gaza bin ka'idojin wannan horo, hukumomin da suka dauke su aiki suna da dokokin daukar mataki".
"Shugaban kasa ya bi doka ta hanyar bai wa 'yan sanda umarni a gudanar da bincike kan wannan abin kaico," in ji Garba Shehu.
Ya kara da cewa shugaban kasar ba ya fuskantar wata barazanar tsaro sakamakon wannan hatsaniya.
Shi dai Sabi'u Yusuf dan uwa ne na jini ga shugaba Buhari kuma akwai dadaddiyar rashin jituwa tsakanin Aisha Buhari da dangin mijinta.
Tun da farko ita uwar gidan shugaban kasar ce ta soma yi kira cewa babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya saki jami'an tsaron da ke kula da lafiyarta.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari