'Yan adawan Mali sun ki shiga gwamnati

Shararren malamin Islama na Mali Mahmoud Dicko da Kawancen adawan kasar sun yi fatali da tayin da shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita ya yi na kafa gwamnatin hadin kan kasa. Maimakon haka sun nemi IBK ya yi murabus.

A ranar Talatar da ta gabata ce Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boukacar Keita ya yi wa jagororin kawancen masu adawa da mulkin nasa tayin kafa gwamnatin hadin kan kasa domin yayyafa ruwa ga wutar rikicin siyasar da ke ci a yanzu haka a kasar da kuma kawo karshen yaje-yajen aiki da malaman makaranta suka share sama da watanni bakwai suna yi. Sai dai kawacen kungiyoyin na M5-RFP wato mouvement du 5 Juin rassemblement des forces Patriotique wanda ya hada kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na addinai da jam'iyyun siyasa a karkashin jagorancin shahararren malamin addinin Islama na kasar Mahmoud Dicko ya ce tayin a kai kasuwa.

Imam Oumaru Diarra shi ne kakakin Imam Mahmoud Dicko jagoran masu adawa da mulkin na Shugaba IBK: Ya ce " Muna nan a kan matsayinmu. Ba mu roki shiga wata gwamnati ko neman tattaunawa da ita ba. Shugaban kasa ya san sarai bukatunmu da kuma burinmu. Domin mun gabatar da su a gaban kafafen yada labarai na gida da na ketare. Kuma magana dai ce ya yi murabus kawai, a cikin laluma domin ci gaban kasar Mali".

 'Yan adawa sun zargi shugaban Mali da gazawa

Sannu a hankali kawancen masu adawa da mulkin shugaban IBK na kara samun goyon baya daga manyan 'yan siyasar kasar inda a baya bayan nan tsohon firaministan kasar Modibo Sidibe da tsohon ministan cikin gida Janar Moussa Sinko Coulibaly da ma tsohuwar gwamnar birnin Bamako Sy Kadiatou suka yi mubayi'a gareshi. Dukkansu na zargin Shugaba Ibrahim keita da nuna gazawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da na tattalin arziki da suka dabaibaye kasar shekaru da dama. Babarou Bocuoum na daga cikin kusoshin jam'iyyar SADI ta shahararren dan adawar kasar Oumar Mariko mamba a kawancen adawa da mulkin na shugaba IBK, ya ce shiga gwamnatin wata gwamnatin hadin kan kasa tamkar yin karan tsaye ne ga dimukaradiyya:

Babarou ya ce " A zahiri shiga wata gwamnatin hadin kan kasa keta haddin dimukuradiyya ne da rena kokowar da 'yan kasa ke yi ta neman kawo sauyi. Domin a zahiri take a yau cewa shawarar shugaban kasa ba za ta samun karbuwa ba domin kasar ta shiga wani hali da ke bukatar a zauna a tantance bukatar da kowane rukunin na al'ummar kasar ke da".

Ko ma dai mi ake ciki za a iya cewa tsugunne tashi ba ta kare wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ba, domin kuwa a wata fira da Imam Mahmoud Dicko jagoran masu adawa da shi ya yi a ranar laraba da manema labarai, ya sake yin fatali da tayin shugaban kasa na kafa gwamnatin kasa da kuma jaddada bukatar ganin ya yi murabus. Hasalima ya sake kira ga 'yan kasar ga su fito a ranar Jumma'a domin sake gudanar da kasaitacciyar zanga-zanga wacce malamin ya kira ta a yi ta ta kare wai ramamme ya zagi maye, yana mai cewa idan har Shugaba IBK ya ki jin bari to kuwa zai ji hoho.

Yanzu dai 'yan kasar ta Mali da dama ne suka zura ido su ga ko zababben shugaban kasar mai shekaru 75 da kuma ke kan wa'adinsa na biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya halitta masa, zai ba da kai bori ya hau, ko kuma zai ci gaba da yin kememe a kan mulkin nasa har sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.

Rahotun DW-Hausa

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN