Wannan bukata dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta gabatar ga kwamitin da ke kula da yaki da cutar Polio a duniya, sannan ta samu amincewar 'yan kwamitin a wani abun da ke zaman matakin karshe a kan hanyar kare shan Inna. Najeriya ta share tsawon wattani har 45 ba tare da samun cutar Polio ba tun bayan irin ta ta karshe a Munguno a shekara ta 2017.
Dr Ehinare Osagie na zaman ministan lafiyar tarrayar Najeriya wanda ya ce sabon matakin na zaman na kan gaba a kokarin kai karshen cutar da a baya ta dauki hankali sakamako na adawa daga mafi yawan al'umma a kasar.
Ya ce “Mun cimma gaggarumin ci gaba, kuma ci gaban shi ne: yanzu mun zama kasar da Hukumar Lafiya ta Duniya za ta ayyana a matsayin wadda ba ta da cutar shan'Inna cikinta. Wannan na da muhimmancin gaske domin kuwa mun dauki lokaci muna aiki tukuru domin kaiwa wannan matsayi, mun wuce shekaru uku da ake bukatar ganin ba'a samu cutar a kasarmu ba. Wannan yana nufin cewa mun fita a cikin ajin mara kyau na kasashen da ke dauke da cutar ta Polio. To sai dai kuma sai a watan Agusta ne muke shirin kawo wa shugaban kasar shaidar fitar da ke da tasirin gaske”
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari