• Labaran yau


  PDP ta yi wani babban kamu a jihar kudu sakamakon rikicin APC

  Gwamna Obaseki ya bayyana shiga jam'iyyar ta PDP ne ranar Juma'a da rana a sakatariyar jam'iyyar da ke Benin, babban birnin jihar, kamar yadda PDP ta wallafa a shafinta na Twitter.

  Ya fitar daga jam'iyyar ne kwana kadan bayan ya fice daga jam'iyyar APC wacce a cikinta aka zabe si a karon farko.

  Gwamnan ya ce ya shiga PDP domin "na samu cimma burina na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo."

  A makon da ya wuce ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

  Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin rikicin ubangida da yaronsa da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Adams Oshimohle kuma shugaban APC da kotu ta dakatar ne ya yi sanadin hana shi sake takara.

  Ranar Talata Gwamna Obaseki ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja yana mai cewa zai koma wata jam'iyyar domin neman takara a wa'adin mulki na biyu.

  A makon da ya wuce ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

  Rahotun BBC


  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: PDP ta yi wani babban kamu a jihar kudu sakamakon rikicin APC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama