Gwamnan jihar Osun Adeboyega Oyetola ya bayar da kyautar motocin alfarma kirar Toyota Jeep guda 13 ga Alkalan babban Kotunan jihar domin tabbatar da gunar da ayyukansu cikin sauki.
NAN ta ruwaito cewa Gwamnan ya mika makullan motocin ga Alkalan a Gidan Gwamnati.A nashi jawabi bayan karbar makullan motocin, babban Jojin jihar Osun Jastis Adepele Ojo, ya yaba wa Gwamnan da ya cika aklawarisa ga sashen shari'a na jihar.
Ya kara da cewa za a yi amfani da motocin ne domin gudanar da ayyukan sashen shari'a yadda ya kamata.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
LABARI