A yayin da tawagar wasu gwamnoni suka jewa iyalan marigayi Tsohon
gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ta’aziyyar rashinshi da aka yi
an samu wata ‘yar Dirama.
Matar marigayin, Madam Florence ta caccaki
mataimakin gwamnan jihar, Mr. Rauf Olaniyan inda ta bayyana cewa mutum
dai mai tsoron Allah ya kamata idan an yi rasuwa irin wannan ko a wayane
ya kira yayi gaisuwa
Tace ko kai ma ya kamata ace ka kira a waya ka maja ta’aziyya. Saidai yace mata ya kira ba’a sauka ba.
Ta
mayar masa da cewa me yasa bai aiko da sako ba tunda bata da lambar
wayarsa, kuma ita matar dan siyasa ce ba zata rika daukar lambobin wayar
da bata sani ba.
A karshe dai tace mijinta ya bautawa jihar kuma ya mutu, kuma kowa ma zai mutu.Gwamnan
Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje dake wajan da sauran gwamnoni sun saka
baki inda suka baiwa duka bangarorin biyu baki akan a yi hakuri.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI