Duba amfanin motsa jiki ga tsoffi

Tsugunar da tsofi a gida da kuma É—auke musu dukkan ayyukan gida kacokan da niyar hutar da su al'ada ce da babu alfanu cikinta ga lafiyarsu.

Yana da muhimmancin gaske a bar waɗanda shekarunsu suka miƙa su ci gaba da ayyukan gida da ba su da haɗari, kamar wanki, wanke-wanke, share-share, goge-goge, tattaki da dai sauransu.

Idan ma son samu ne, bayan ayyukan gida ana so su ɗinga yin atisaye da ba zai gaza na minitina 30 kullum ba. Irin atisayen da suke buƙata sune:

i. atisayen bunƙasa / inganta aikin zuciya, jijiyoyin jini, huhu da ma garkuwar jiki gaba ɗaya.

ii. atisayen ƙarfafa tsokokin jiki da ƙara kuzari.

iii. atisayen bunƙasa daidaiton jiki.

Duk waÉ—annan atisaye za su temaka wajen rage haÉ—arin kamuwa da ciwon siga, hawan jini, ciwon daji  kansa da sauran cutukan da kan zo yayin tsufa kamar matsalolin rashin bacci, damuwa, ruÉ—ewa, gigi da larurar kyarma.

Haka nan, atisaye zai temaka wajen rage afkuwar babbar matsalar nan ta faɗuwa ga tsofi, wannan matsala ce da kan haifar da haɗura kamar rauni, targaɗe, gocewar gaɓa, wani lokacin ma har da karaya.

Har wa yau, kasancewarsu cike da ƙwarin jiki da kuzari zai sake rage haɗuran faɗawa cikin haɗura kamar ƙunan wuta, kaɗewar abun hawa da sauransu.

Saboda haka, tsugunar da tsofi a gida ba tare da motsa jiki / atisaye ba na da haÉ—arin karya garkuwar jikinsu, dalilin da ya sa cutuka kamar cutar korona ke saurin lashe rayukansu.

Phusio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN