Ali Nuhu ya ce bayan ya kammala karatun sakandare ya rubuta jarabawar JAMB ya kuma samu gurbin karatu a fanin hada magunguna (Famasi) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), amma sai ya ki zuwa ya yi karatun saboda burinsa na zama dan fim.
“Ni a lokacin burina shi ne na yi karatu a Jami’ar Jos domin a nan ne nake da damar koyon fim, don haka sai na ki karbar gurbin karatun da aka bani a ABU.
“Da mahaifi na ya ji matakin da na dauka sai ya ki yarda, domin yana ganin na samu gurbin karatu kai tsaye da zan yi karatun digiri a Famasi, a ABU, ya yi min hangen cewa Famasi karatu ne mai mahimmanci.
“Ni kuma dalilina na kin karatun shi ne a ABU ba zan samu damar haduwa da kwararru a harkar fim ba, don haka ne na so na je Jos domin a lokacin ita ce cibiyar masu shirya fim a Arewa.
“Ba na son bacin ran mahaifina, sai na yi ta ba shi hakuri. Shi abin da yake jiye min, idan na je Jami’ar Jos zan koma baya domin sai na faro daga matakin share fagen shiga jami’a.
“Ni kuma sai na gwammace na koma baya domin na cimma burina na shiga harkar fim, a haka mahaifina ya hakura, ya yarda na tafi Jami’ar Jos”, inji Ali Nuhu.
‘Na hadu da kwararru a harkar’
Ya ce a lokacin karatunsa a Jami’ar Jos da ke jihar Filato ya samu damar haduwa da kwararrun masu shirya finafinai na wancan lokacin. Ya ce yakan je Gidan Talbijin na Kasa da ke garin Jos domin neman sanin makamar aikin wasan kwaikwayo.
“Dama tun ina karami ni mutum ne mai yawan kallon talbijin, idan ina kallon masu karanta labarai suna burge ni kwarai”, inji shi.
Jarimi Ali Nuhu ya bayyana haka ne a hirarsa da wani kamfani da ke samar wa matasa aikin yi tare da ba su shawarwari.
Kamfanin ya gayyaci Ali Nuhu ne ya kuma zanta da shi ta kafar sadarwa ta bidiyo don ya ba wa matasa tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayar da ya sha domin su amfana da matakan da ya bi ya cimma burinsa.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari