• Labaran yau


  Dan Najeriya yayi tsalle daga bene hawa na 9 don kaucewa kamun jami’ai a Indonesia

  Wani dan Najeriya dake zaune a kasar Indonesia ya fado daga dogon gini mai hawa 27 inda yayi tsalle daga hawa na 9 don gujewa kamun jami’an tsaoro.

  A cewar rahotanni, lamarin ya faru ne da safiyar yau a Gadin Nias, Jakarta, dake kasar Indonesia.

  Rahotanni sun nuna cewa mutumin da ba a bayyana sunan shi ba yana kokarin tserewa jami’an kula da shige da fice wadanda suka kutsa cikin ginin don kamo bakin hauren dake zaune ba tare da takardun izinin zama ba a kasar.

  Sai dai an bayyana mutumin ya sami raunuka kaɗan kuma an garzaya da shi zuwa wani asibiti dake kusa.

  ‘Yan Najeriya dadama.na fuskantar barazanar kamu daga Jami’an kula da shige da fice dake kasar Indonesia wanda hakan ke jefa rayukansu cikin hadari.

  Hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan Najeriya yayi tsalle daga bene hawa na 9 don kaucewa kamun jami’ai a Indonesia Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama