Kotu a jihar Borno ta daure wani tsohon ma'aikacin ma'aikatan shari'a na jihar tsawon shekara 8 sakamakon damfarar Zawarawa 194.
Wanda Kotu ta kama da laifi mai suna Ramat Muhammed, wanda aka fi sani da suna Gaddafi, an daure shi sakamakon damfara Zawarawa 194 adadin kudi har N781,800.00.
An kama Ramat da laifin amfani da katin bogi na izinin sayar wa matan da abinci da sunan kungiya mai zaman kanta NGO , alhali ba gaskiya bane.
Haka zalika Alkalin Kotun Umaru Fadawa, ya umarci Ramat ya mayar ma wani Makarantar Fisabilillahi adadin kudi N781,800.00.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari