Tsawa ta fada wa ofishin jami'an FRSC na Itele-Ijebu da ke kan hanyar Ijebu-Ode-Ore ta kuma kashe mutum uku ta watsar da sauran mutane a kasa ranar Laraba 17 ga watan Yuni da sanyin safiya.
Lamarin ya faru da misalin karfe 10 na aafe a tsohon Toll gate na tagwayen hanya, wanda haka ya jefa rundunar jamai'an FRSC na jihar Ogun cikin alhini.
Mun samo cewa jami'an suna kokarin gudanar da paretin safe da aka saba a harabar ofishinsu, sai tsawa ta fada masu. Nan take mutum 3 suka mutu , saura kuma suka fadi sakamakon radadin wutan lantarki da tsawar ta watsa masu wanda ya shafi fiye da mutum 12.
Jami'in wayar da kan al'umma da fadakarwa na rundunar FRSCna jihar Ogun Florence Okpe ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ki ya ce uffan ko karin bayani.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari