Gwamnatin tarayyar Najeriya ta saki fursunoni 6,590 da ke tsare a gidajen gyaran hali daban daban a sassar kasar. Hakan na kunshe ne cikin wani rubutu da Attoney Janar na kasa, AGF, kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 17 ga watan Yuni.
A cewar Malami, fursunonin sun cika ka'idojin da aka gindaya na sakin fursunoni daga gidajen gyaran hali 32. Ministan yayin da ya ke gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu daga 2015 zuwa 2020 ya ce ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a wasu jihohi 14. Idan za a iya tunawa,
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a bullo da hanyoyin gaggauta sharia da rage cinkosu a gidajen gyaran hali a kasar sakamakon bullar annobar coronavirus. Fadar shugaban kasar ta bakin mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu.
Shugaban na Najeriya a wasikar da ya aike wa Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad ya tunatar da shi rokon da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ga kasashe su rage cinkoso a gidajen gyran hali na kasashensu don samar da tazara.
A wani labarin, kun ji cewa wasu kananan yara biyu da ba a ambaci sunansu ba sun rasa rayyukansu a ranar Laraba bayan gini ya rufta a kansu a Gafari Balogun na Ogudu da ke jihar Legas. Shugaban Hukumar
Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi. Ya kara da cewa wadanda suka mutu kananan yara ne kuma an ciro gawarwakinsu daga baraguzan ginin.
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari