Sojin kasar Faransa sun halaka shugaban kungiyar Al'qaeda na arewacin Afrika da yankin Maghreb Abdelmalek Droukdel bayan shekara bakwai ana nemansa ruwa a jallo.
Sojin Faransa sun halaka shi tare da wasu na hannun damansa kuma manyan Kwamandodinsa a wani farmaki da suka kai ranar Laraba a kasar Mali.
Faransa ta tura dubban sojinta zuwa kasar Mali domin yaki da kungiyar Al'Qaeda da ke ci gaba da wanzar da aikinsu na kashe kashen bayain Allah a kasar Mali da yankin Maghreb.
Ministan tsaro na kasar Faransa Florence Parly ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
LABARI