Ababe 10 da ya kamata ka sani dangane da Abubakar Dutsin Mari babban ma'aikaci a Kebbi

Daya daga cikin fitattun mutanen kirki, daga cikin manyan ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi da halayensu ya amanantar da yardar jama'a garesu shine Abubakar Dutsin Mari, wanda shi ne Sakataren din din dim a ma'aikatar kudi na jihar Kebbi a halin yanzu.

Sakanakon wani takaitaccen bincike da Mujallar ISYAKU.COM ta gudanar ya nuna cewa Dutsin Mari ya yi zarra daga cikin Sakatarorin din din dim da ake da su a jihar Kebbi ta wasu fannoni bisa alkalummar da muka tattaro.

NAGARTATTUN HALAYENSA


A. Bayar da kyautuka ba tare da nuna bangaranci ba
B  Taimakon ma'aikata a ko ina a jihar Kebbi
C. Saukin tafiyar da aiki
D. Hakuri da yanayin jama'a na wajen aiki da na ma'amalan yau da kullum,
E. Bayar da taimako ga mabukata ko kafin mabukaci ya tambaye shi,
F. Darajanta kowa har da wadanda ya zarce masu a shekaru.
G.Biyayya ga na gaba da shi tare da martaba su.
H.Sa bukatun ma'aikatan Gwamnati da jama'a gaba da nashi bukatun.
I.  Riko da gaskiya tare da aiki da shi.
J. Tausayawa tare da sauwakawa lamarin ma'aikata da jama'a.

Hakazalika binciken mu ya nuna cewa Abubakar Dutsin Mari ya zagaya kusan gaba dayan jihar Kebbi ta Masarautun jihar wajen aikin Gwamnati, domin ya yi aiki a kananan hukumomi 19 cikin kananan hukumomi 21 da ke jijhar Kebbi.

MUTUNCI DA YA JAWO MASA MARTABA GA MA'AIKATAN JIHAR KEBBI

Dutsin Mari ya fito da tsarin martaba ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi masu kwazo wajen tafiyar da aikinsu, kamar yadda ya tabbata lokacin da yake Sakataren dindindin na Gidan Gwamnatin jihar Kebbi.

Dutsin Mari ya martaba wadanda suka cancanta su sami kyautar yabo saboda sadaukar da kansu da suka yi wajen tafiyar da aikin Gwamnati. Lamari da ba a faye samun Sakatarorin din din din suna yi ba a jihar Kebbi.

YA SAMI AMINCEWAR ZUKATAN JAMA'A

Dutsin Mari ya sami amincewar talakawa, ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi, kasancewa ya san makaman aiki domin ya yi hulda da jama'a da dama a tsawon rayuwarsa na aikin Gwamnatin jihar Kebbi, ta hanyar aikatuwa a kananan hukumomi 19 cikin 21 da ke jihar.

Isyaku Garba Zuru.

Mawallafin mujallar ISYAKU.COM

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN