Type Here to Get Search Results !

Main event

Yunkurin gwamnan jihar Edo na sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP ya fara kawo matsala a cikin tafiyar PDP.

Yunkurin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki na sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP ya fara kawo matsala a cikin tafiyar PDP.

Wasu manyan jam’iyyar adawar su na nuna mabanbanta ra’ayo game da kokarin mikawa gwamnan tikitin takara.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa yayin da gwamnonin PDP su ke goyon bayan a ba Godwin Obaseki tikitin jam’iyya, wasu jagororin PDP a jihar Edo su na ganin cewa hakan zai bata tsarin jam’iyya.

Tsofaffin jiga-jigan PDP a jihar Edo sun fara nuna rashin jin dadinsu a game da yadda ake fifita Obaseki a wajen takarar gwamnan da za a yi.

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa gwamna Ifeanyi Okowa oda sanatocin jihar Edo: Clifford Ordia da Urhoghide Aishagbonnriodion su na cikin masu kokarin ganin cewa PDP ta tsaida Godwin Obaseki a matsayin ‘dan takararta.

Manyan PDP a yankin irinsu Nyesom da Dan Orbihe ba su tsoma baki game da lamarin ba tukuna.

Ko da Godwin Obaseki ba zai samu damar neman tikiti a APC ba, har yanzu bai bayyana matsayarsa game da sauya-sheka ko matakin da zai dauka.

Kafin Obaseki ya sauya-sheka zuwa PDP, akwai sharudan da za a gindaya tsakaninsa da jam’iyyar domin a tsaida shi a matsayin ‘dan takara.

Daga cikin sharudan da za a bada shi ne: Ba Godwin Obaseki takardar zama ‘dan jam’iyya da tsaida shi a matsayin ‘dan takara ba tare da hamayya ba.

Sauran sharudan sun hada da: Phillip Shuaibu ba zai samu kujerarsa ta mataimakin gwamna ba. Babu maganar Obaseki ya koma jam’iyyar APC idan PDP ta lashe zabe.

Sannan kuma dole magoya bayan gwamnan su narke a PDP, kuma Obaseki ya tafi da ‘yan PDP a gwamnatinsa. Haka zalika ka da komawarsa PDP ta kawo rigima.

Rahotun Legit


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies