Rashin kwarewa da mugayen fadawa su ne matsalar Buhari’

Furofesa Ango Abdullahi shi ne tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya wanda kuma yanzu shi ne Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa.

A hirarsa da Aminiya ya zargi Shugaba Buhari da nuna gazawa da kuma kewaye kansa da kuraye wanda hakan ya sa gwamnatinsa ta kasa katabus.

Aminiya – Najeriya tana murnar cika shekaru 21 da komawa mulkin damokuradiyya, ko mene ne ra’ayinka?

Furofesa Ango Abdullahi – Ni ban yarda cewa ranar 29 ga watan Mayu ce Ranar Damokuradiyya ta Najeriya ba. Ranar Ramokuradiyya ta Kasa ita ce ranar 1 ga watan Oktoba na kowace shekara, domin a wannan rana Najeriya ta samu ‘yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka.

Amma idan Ranar Damokuradiyya na nufin ranar da muka bar tsarin mulkin soja muka koma na siyasa ne, to ni ina ganin abin da muka yi shi ne mun bar mulkin soja ne muka koma na farar hula. Ka kuwa san akwai bambanci tsakanin mulkin damokuradiyya da na farar hula.

Amma ni a ra’ayina kawo yanzu babu wani abin da muka amfana da shi tsawon shekaru 21 din nan na dawowar mulkin damokuradiyya. Kai a yanzu ne ma cikin wadannan shekaru biyar ko hudu muka fi ganin tasku a duk cikin shekaru 21 da aka shafe ana mulkin damokuradiyya.

Yaya kake kallon salon mulkin shugaba mai ci, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yanzu?

To, abu ne mai wuya a iya amsa wannan tambaya kai tsaya. Daga nesa, zan iya cewa ya dauki wasu muhimman mukamai ya ba wasu wadanda ba su san makamar aiki ba. Sannan suna ta dambarwa sun kasa aiwatar da aikin.

Duk wani karfin iko kundin tsarin mulkin kasa ya ba wa shugaban da aka zaba ne kamar Buhari. Saboda haka abin da kawai zai yi shi ne ya aiwatar da ikon nasa don biyan muradun jama’ar kasa.

Tabbas ba zai iya yin komai shi kadai ba, mun yarda da haka. Amma dole ne ya samo wa kansa kwararrun mutane ya basu wasu ayyukan da yake nasa ne.

‘Yan watanni bayan an zabe shi na taba fadar cewa tabbas mun aminta da gaskiyarsa, to sai dai ya kasa samo abokan aiki na kwarai da zai nada a ministoci da sauran mukamai, wadanda da su ne zai iya aiwatar da ayyukansa a matsayinsa na Shugaban Kasa.

A matsayinka na malamin makaranta, idan aka ce ka ba wa Buhari maki a jerin shugabannin da aka yi a baya tun dawowar damokuradiyya, nawa za ka bashi?

A cikinsu da shugaban kasa daya tal na taba yin aiki. Na yi aiki da Obasanjo na tsawon shekaru uku. Kuma tabbas Obasanjo nagartaccen shugaba ne.

Na tabbatar da Obasanjo ya fi Buhari nagarta sosai saboda Obasanjo yana daukar gabarar nauyinsa a matsayinsa na Shugaban Kasa ko da kuwa daidai ne ya yi ko kuwa kuskure.

Wuyar aikin Shugaban Kasa shi ne daukar matakin da ya dace. Matakan na iya zama daidai ko kuskure. Amma dai mafi muhimmanci shi ne ya kasance ya dauki matakin a matsayin aikinsa ne.

Shi yana daukar mataki da nauyin daukar matakin. Wannan shi ne babban bambanci tsakanin shugabancin Obasanjo da Buhari.

Bacin sa mutanen da ba su cancanta ba a mukamai, wane abu ne kuma kake ganin ya sa Gwamnatin Buhari ta kasa katabus?
Ka san ni ban taba kasancewa kusa da shi ba, amma dai daga nesa zan iya cewa akwai rashin jajircewa. Jajircewa na nufin ya fito a matsayinsa na shugaban kasa ya tabbatar duk wani mataki da ya dauka an aiwatar da shi har zuwa karshe.

Amma mun fuskanci cewa ba shi da wannan jajircewar. Misali, idan aka zargi wani na kusa da shi da yin almundahana ko wani laifi kuma ka bukaci a kawo maka sheaida kuma aka gabatar maka; ya dace shugaban kasa ya dauki mataki a kansa. Amma yanzu akasin hakan ake yi.

Muna da misalan mutanen da ake da zarge-zarge a kansu kuma aka gabatar da shaidu a kansu, amma duk sun sha. Ina magana kan cin hanci da rashawa ko kuma aikata wani abin kunya ne.

Zai yi wuya jama’a su iya tantance wadannan matsayinka guda biyu, ganin cewa kana daya daga cikin manyan mutane da suka rika yi wa Buhari kamfe a shekarar 2015.

Abin da ya kawo haka shi ne mun yi zaton zai yi aiki sosai domin abubuwa sun kazance a wancan lokaci. Wani babban abu kuma shi ne rashin cika alkawarin yarjejeniya da PDP ta yi wanda na san ita jam’iyyar suna sane.

Akwai yarjejeniyar cewa bayan Obasanjo ya gama shekarunsa takwas, za a kawo dan takara daga Arewa wanda zai shugabanci kasar tsawon shekaru takwas. Amma cikin rashin sa a, sai Umaru ‘Yar’adua ya rasu bayan ya share shekaru uku kan karagar mulki.

Ka ga wannan na nufin akwai sauran shekaru biyar na ‘yan Arewa amma saboda mutuwar ‘Yar’aduwa sai hannun agogo ya koma baya. Don haka mun yi tsammanin jam’iyyar za ta tsayar da wani dan Arewa ne a 2011 ba tare da kace-nace ba koda kuwa a wata jam’iyyar ne daban.

To da muka ga PDP ta ki mutunta wannan yarjejeniyar ne sai muka goya wa Buhari baya don muna tsamnanin a wancan lokacin ya fi kowanne dan takara cancanta.

A zaben 2015 da na 2019, Buhari ya dora kamfe dinsa a kan muhimman abubuwa uku; tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arzikin kasa. Kana nufin bai tabuka komai ba a wadannan abubuwa?

E to, ta fannin tattalin arziki dai kai zan tambaya yaya kake ji da cefane yanzu? Maganar rashin tsaro kuwa wani abu ne mai daure kai, domin a lokacin da ya karbi mulki babbar matsalar da ake fama da ita ita ce matsalar Boko Haram. Yanzu ga ta ‘yan bindiga da ta masu kama mutane don karbar kudin fansa da sauran matsalolin tsaro da ta kai mutane a gidajensu suna aikata laifuka.

Bayan mun yi nazarin duk wadannan ne muka ga bai dace a sake zabar sa a karo na biyu ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka ba wa ‘yan Najeriya shawarar kada su sake zaben sa a karo na biyu, domin ya nuna gazawarsa a fili kan magance wadannan kalubalen da suke ta karuwa kullum.

Wannan matsayi namu a 2019 ya jawo cece-kuce da zarge-zarge, amma yanzu duk kowa yana gani a zahiri abin da muka hango a 2019 cewa Buhari ba iya magance mana matsalolinmu ba.

Mene ne mafita a shawararka?

An sha ba shi shawara cewa mutanen da ya dora wa alhakin samar da tsaro ga ‘yan Najeriya sun kasa inganta. Yanzu mutane ne za su alkalanci kan shin gwamnatin na daukar shawarwarin da ake ba ta.

Duk da haka ina ganin Buhari na da sauran dama domin akwai sauran shekara uku kafin cikar wa’adinsa. Abin da ya rage shi ne ya tunkari aikin da ke gabansa haikan sannan ya nada mutanen da suka dace don yi masa wannan jan aiki. Na san har yanzu akwai ‘yan Najeriya da yawa masu irin nagartar da ake bukata.

Yanzu idan aka nemi ka zo ka taimaka da irin basirara da kwarewarka za ka taimaka?

Sam. Allah ya tsari gatari da saran shuka.

Me ya sa?

Saboda ba na aiki da jita-jita, dole sai na ma tabbatar da dalilin da zai sa a gayyace ni kafin ma in duba yuwuwar amincewa ko akasin haka.

Amma duk da haka yana da kyau mu fahimci cewa ba wata kasa da za ta cigaba ba tare da nagartaccen shugabanci ba. Ka je ka binciki tarihi; duk kasar da ka ga ta samu cigaba, to ba shakka shugabanci na gari ne ya haifar mata da shi. Da zarar ka sami shugabanni na gari, to tabbas za ka sami shugabanci mai nagarta wanda shi kuma shi yake haifar da gaskiya, rikon amana da kuma fatattakar rashawa. Amma matukar mu ka gaza samun wannan, to tabbas mu da maganar cigaba sai dai mu ji a salansa.

Ya kamata kuma Najeriya ta sake duba na tsanaki kan irin tsarin mulkin da take gudanarwa a yanzu haka. Tsarin shugaba mai cikakken iko da muka kwafo daga Amurka yana da tsada sosai kuma bai dace da kasashe masu tasowa irin Najeriya ba.

Kamata ya yi mu koma Kam tsarin mu na farko na shugaban kasa da fira-minista. Shi tsarin shugaba mai cikakken iko ya baiwa shugaba iko fiye da kima kuma yana taimakawa wajen kama karya.

 Rahotun Jaridar Aminiya

AGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN