Type Here to Get Search Results !

Main event

Mutuwar kwamishina ta sa gwamna killace kansa

Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya killace kansa saboda fargabar bullar cutar COVID-19 a fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Ikpeazu da mataimakinsa Ude Oko Chukwu da sauran ‘yan Majalisar Zartarwar jihar na killace kansu ne bayan iyalen jagoran yaki da cutar COVID-19 a jihar Marigayi Solomon Ogunji sun kamu da ita.

Mista Ogunji shi ne kuma kwamishinan muhalli na jihar.

Ya rasu ne a makon jiya sakamakon rashin lafiya mai nasaba da hawan jini, a cewar Kwamishinan Yada Labaran jihar Chief John Okiyi Kalu.

Raswuar Mista Ogunji ta sanya fargaba yiwuwar cutar coronavirus ce ta yi ajalinsa.

Hakan ce ta sa aka dauki jinin iyalen mamacin domin yi musu gwajin cutar.
Sakamakon gwajin da ke nuna iyalen mamacin sun kamu da cutar  na ci gaba da haddasa damuwa.

Gwamna Ikeazu da ‘yan Majalisar Zartaswarsa da ‘yan kwamitin ministoci da wadanda suka yi mu’amala da Ogunji za su kasance a killace na tsawon sati biyu.

Kwamishinan Yada Labaran jihar ya kara da cewa gwamnan ya umurci dukkannin wadanda suka yi mu’amala da mamacin da su gabatar da kansu domin a yi musu gwajin cutar.

Kafin yanzu mutum biyar ne kacal suka kamu da coronavirus a jihar Abia.

Daga cikinsu mutum biyu da suka fara kamuwa  sun warke.

Rahotun Aminiya

AGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies