Har wa yau, sanya jakar 'wallet' a aljihun baya, musamman yayin dogon zama, na iya danne ko shaƙe wata babbar jijiyar laka da ake cewa 'sciatic nerve' a turancin likita. A yayin da aka danne wannan jijiyar laka tsawon lokaci zai kawo sagewa, zogi, dindiris, rauni ƙafa da kuma saukar ciwo zuwa ƙafa, abin da a likitance ake cewa 'wallet sciatica'.
Kauce wa sanya jakar 'wallet' a aljihun baya musamman yayin dogon zama don kauce wa danne wannan jijiyar laka da ma matsalolin da ke biyo baya.
Idan ka ci gaba da jin waɗannan matsaloli bayan ka daɗe a zaune sanye da jakar 'wallet' cikin aljihunka na baya, tuntuɓi likitan fisiyo da wuri don magance matsalar.
Daga shafin Physio Hausa
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari