Matsalar Ƙwacewar fitsari da abin da ya kamata mace ta yi

Ƙwacewar fitsari matsala ce ruwan dare da ba a cika neman maganinta ba saboda kunya, tsoron tsangwama ko kuma zaton cewa ƙwacewar fitsarin wata sananniyar al'ada ce musamman ga mata yayin rainon ciki da bayan haihuwa.

Ƙwacewar fitsari matsala ce da ke barazana ga ibada, walwala, tsabtar jiki da kuma ingancin rayuwar masu fama da ita.

Matsalar ƙwacewar fitsari na shafar maza da mata sai dai ta fi shafar manyan mutane. Haka nan, matsalar ta fi shafar mata manya, inda take shafar kimanin mata kaso hamsin cikin ɗari (50%) da kuma maza kaso goma sha ɗaya cikin ɗari (11%). Sai dai kaso ashirin da biyar zuwa sittin da ɗaya cikin ɗari (25–61%) ne kawai na matan ke iya samun kulawa.

Daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin gamuwa da ƙwacewar fitsari akwai:

1. Jinsi: jinsin mata sun fi maza samun matsalar.

2. Rainon / goyon jiki da haihuwa.

3. Doguwar / tangarɗar naƙuda.

4. Ƙiba

5. Matsanancin tari tsawon lokaci.

6. Raunata jijiyoyin laka na baya.

7. Shan taba sigari.

8. Tiyatar ƙugu / mafitsara, da sauransu.

Ƙwacewar fitsari yayin ayyukan yunƙuri kamar ɗaga nauyi, dariya, tari, atishawa ko motsa jiki matsala ce da ke faruwa sakamakon raunin / rashin ƙwarin tsokokin da ke shimfiɗe a ƙasan ƙugu. Waɗannan tsokoki sune ke riƙe da maɗaurin jakar mafitsara. Saboda haka, raunin tsokokin zai riƙa haifar da ƙwacewar fitsari ba tare da sanin mutum ba. Irin wannan ƙwacewar fitsari ana kiran sa da 'Stress Urinary Incontinence' a turance.

Saboda haka, idan kina da ƙorafin ƙwacewar fitsari ba tare da saninki ba, musamman yayin da kika yunƙura domin zama, miƙewa, ɗaga kayan nauyi, dariya, tari ko atishawa to alama ce ta wannan matsala.

Kada ki bari kunya ko tsoron tsangwama su hana ki bayyana damuwarki. Tuntuɓi likitan fisiyo a yau don ɗora ki kan hanyar da za ki yi bankwana da matsalar ƙwacewar fitsari.

Daga shafin Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN