Mata ta lalata al’aurar Mijinta bisa zargin cin Amana

Hukumar Civil Defence ta jihar Osun ta bayyana cewa ta samu korafi akan wata mata data lalatawa mijinta Al’aura bisa zargin da take masa yana cin amanarta.Me magana da ywun Hukukmar Civil Defence na jihar,

Daniel Adigun ne ya bayyana haka inda yace wata mata, Omolara Seriki ce ta kai musu korafin mijinta cewa baya kula da ‘ya’yansu hakanan baya bata hakkinta a matsayin matarsa.Saidai da aka tuhumi mijin sai ya bayyana cewa shekarar su 6 da aure amma matarnan baya hin dadin zama da ita duk da suna da yara 2.

Yace ya gaji da cin zarafin da take masa shiyasa ya bar mata gidan ya koma gefensa can da zama. Wata rana wata tazo kaimai abinci sai ruwan sama ya fara, dan hakane ta tsaya ta fake.

Yace can kawai sai yaji ana kwankwasa kofa, yana budewa sai yaga matarshi ce, tana yin arba da wannan data kawo mai abinci sai fada ya kacame tsakaninsu, nan ta kama mai maraina tana barazanar fizgesu, yace a nanne sai ya suma.

Bai farka ba sai a gadon Asibiti inda aka mai aiki a marainansa.Da aka tambayi matar tace kasheta yaso yayi shiyasa ta mai haka. Ta kara da cewa ta dade tana zargin yana cin amanarta shine rannan taje inda yake tare da wadda yake cin amanarta da ita ta kamashi.

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN