Mahukunta a kasar Rasha sun bayyana kama wani matashi da ya kashe
tsihuwar budurwarsa dan ya tabbatarwa da sabuwar budurwarsa cewa yana
sonta.The Mirror ta ruwaito cewa Alekzey Petrov dan kimanin shekaru 20
ya ja tsohuwar budurwarsa,
Anastasia Pospelova cikin daji inda ya kashe
ta.Petrov da budurwarsa ta yanzu,Karpova sun ja Anastasia daji da cewa
zasu hada casune. Sun kunna euta inda suka fara rawa, a nan ne Petrov ta
fitar da wuka ya cakawa Anastasia a wuya.
Ta yi kokarin guduwa inda har ta kira abokiyarta a waya ta gaya mata amma abokiyar tace tana sha wasa ne take mata.Ta
boye amma Petrov ya gano ta ya kara caka mata wuka a kirji sannan ya
take mata wuya har ta mutu. Sun binne ta a dajin inda suka koma gida
suka ce ta bata.Binciken da ‘yansandan suka kaddamar yasa an gano gawar
Anastasia a daji da alamar yanka a jikinta. Daga ba dai Petrov da
budurwarsa sun amsa laifinsu.Wata majiya ta bayyana cewa Petrov da
sabuwar budurwarsa, Karpova sun sha samun rigima kan zargin da take
masa cewa har yanzu yana son tsohuwar budurwarsa, abinda ya sha musa,
dalilin hakane ma ya sha Alwashin kashe tsohuwar budurwar tasa dandai ya
tabbatar mata da cewa yana sonta.
Da ake neman gawar Anastasia hadda
masoyan biyu akai ta bincike cikin daji, bayan da aka gano ta sun amsa
laifukansu. Idan dai kotu ta tabbatar musu da laifin to zasu fuskanci
hukuncin shekaru 15 a gidan yari.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari