• Labaran yau


  Likitoci sun yi iya bincikensu amma sun gaza gano mabubbugar dadin mata a lokacin jima’i watau G-Spot

  Wasu Likitoci da suka yi bincike akan mata masu matsakaitan shekaru 17 dan gano gurinnan da ake kira da G-Spot wanda da yawa suka yi amannar cewa idan aka tabawa mace shi, to shine kololuwar Ni’imar Jima’i a gareta sun ce basu gano wannan guri ba dan haka ba gaskiya bane babushi.

  Wani likitan mata dan kasar Jamus, Marigayi Ernst Grafenberg ne a shekarun 1950 ya ce ya gano wannan mabubbugar dadin wanda a karshe aka laka ma abin sunansa.

  Bayyanr wannan abu yasa kamfanoni masu yin abubuwan jima’i na Roba ga mata suka kara samun tagomashi sosai inda suke amfani dashi wajan talla.

  Likitocin da suka yi wannan sabon bincike ‘yan kasar Turkiyya ne wanda kuma aka wallafa sakamakonshi a mujallar likitanci kan harkar mata ta Duniya da muka samo Rahoton a Daily Mail.

  Tun bayan Grafenberg Likitoci sun yi ta bayyana cewa wannan abu babushi kawai mafarkine. Saidai duk da haka wani bincike da aka yi ya bayyana cewa wasu matan na kishin cewa basa jin irin dadin da wasu matan ke ji masu G-Spot yayin Jima’I saboda su basu dashi ko kuma ba’a taba tabo musu shi ba.

  Hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Likitoci sun yi iya bincikensu amma sun gaza gano mabubbugar dadin mata a lokacin jima’i watau G-Spot Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama