A ranar Juma’a ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin
gwamnonin APC da suka kai masa ziyarar godiya bayan taron majalisar koli
na jam’iyyar.
Gwamnonin da suka hada dana Ekiti, Kogi da Yobe sun yi
ganawar ne da shugaban a cikin fadarshi, saidai babu wata sanarwa a
hukumance akan tattaunawar tasu.
Saidai wata Majiya daga cikin ganawar ta
shaida cewa shugaban kasar ya baiwa gwamnonin APC umarnin cewa subyi
dukkan mai yiyuwa wajan kwato jihar Edo daga hannun PDP.Shugaban ya
bayyana takaici akan yanda gwamnan jam’iyyar mai ci ya barta zuwa PDP.
Ya kuma ce a yi kokarin tabbatar da cewa jihar Ondo bata fada hannun PDP
ba.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI