Wata yarinya mai matsakaitan shekaru ta bayyana yadda lamarin boko haram ya canja fasalin rayuwarta bayan Kawunta wanda dan kungiyar boko haram ne ya yi ta yi mata fyade.
A wani shirin BBC da aka yi ranar 19 ga watan Yuni, yarinyar ta ce tana makarantar Sakandare na gaba da Framare, kuma tana fatan ta zama Soja, amma sai wannan mumunan lamari ya canja alkiblar rayuwarta.
Ta ce " Wata rana, ranar Talata, yan boko haram suka shigo kauyenmu, suka kashe maza, kuma suka kone gidaje. Daga bisani suka dauki mu sauran mata.
"Kawu na wanda dan kungiyar boko haram ne ya gaya mani cewa in biyo shi, domin yanzu na zama mallakinsa. Tun daga wannan rana ya fara yi mani fyade".
" Duk da yake shi kansa an kashe shi bayan sabanin ra'ayi tsakaninsa da sauran yan boko haram, daga nan kuma sai aka aurar da ni ga wani dan kungiyar ta boko haram".
" Jama'a na yi mana kallon cewa mu matan yan boko haram ne, kamar mu ne muka jawo wa kanmu wannan lamari, sakamakon haka ba zan taba yafe wa yan boko haram ba domin sun illata rayuwata har abada".
"Buri na a yanzu shi ne in zama sojan sama, in tuka jirgin yaki domin in yi wa yan boko haram luguden wuta, domin a halaka su gaba daya a Najeriya". Inji budurwar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari