• Labaran yau


  Mutum 6 sun mutu, gidaje 600 sun rushe bayan ruwan sama da iska mai Karfi a Kano

  Dailytrust ta rawaito cewa mutum shida suka rasa rayukansu baya ga gidaje 600 da suka rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi a kananan hukumomi hudu a jihar Kano.

  Kazalika wasu mutum 1,752 sun rasa muhallansu sakamakon iftila’in a cikin mako guda a jihar, inji Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano.

  Shugaban hukumar Sani Jili ya ce wutar lantarki ta kashe daya daga cikin mamatan, sauran biyar din kuma gini ne ya fada a kansu.

  Sani Jili ya ce iftila’in ya shafi Kananan Hukumomin Gwale, Gwarzo Rimin Gado, da kuma Kibiya ne a cikin a makon jiya.

  Ya ce hukumarsa na jiran rahoton sauran kanana hukumomin da abin ya shafa yayin da ma’aikata ke kokarin tattara alkaluman barnar da aka samu.

  A cewarsa Rimin Gado da Kibiya sun riga sun gabatar da rahotanninsu, har an tallafa musu da kayan rage radadi a matakin farko ga wadanda suka yi asara.

  Kaya da aka rabawa mutanen kai tsaye sun hada da “kayan abinci, tufafi da kayan shinfida, sai kuma buhunan siminti”, inji shi.

  Rahotun Jaridar Alummata

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 6 sun mutu, gidaje 600 sun rushe bayan ruwan sama da iska mai Karfi a Kano Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama