Type Here to Get Search Results !

Kani ya kashe matar yayansa bayan ya yi mata fyade a Gusau jihar Zamfara

Yansanda a jihar Zamfara sun kama wani saurayi mai shekara 25 Aminu Bala, bisa zargin kashe matar yayanshi bayan ya yi mata fyade a Gusau.

Yayin da Kakakin rundunar yansandan jihar Zamfara ya gabatar da shi ga Manema labarai, SP Muhammed Shehu ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa gaban yansanda.

Ya ce wanda  ake zargin dan asalin karamar hukumar Maradun ne a jihar ta Zamfara.

Kakakin yansandan ya ce '  Ranar 15 ga watan yuni, yansandan sashen Tudun Wada dake Gusau suka sami kiran gaggawa da karfe 04.30 na Asuba daga rukunin gidaje na Dambo da ke Gusau cewa wani ya kashe matar yayansa".

" Bisa wannan dalili ne yansanda suka isa wajen kuma suka tarar da Hauwa Illiyasu cikin jini bayan an sassareta da adda. Daga bisani suka kaita babban Asibitin Yariman Bakura da ke Gusau inda Likitoci suka tabbatar da mutuwarta".

Kakakin yansanda ya kara da cewa yansanda sun tuntubi mijin Hauwa ta wayar salula, kasancewa baya cikin jihar, inda ya shaida masu cewa kaninsa ya taba yin barazanar cewa zai kashe matarsa Hauwa.

SP Muhammed ya ce yansanda na jiran isowar mijin Hauwa, domin su sami rubutaccen jawabinsa wanda za su yi amfani da shi a zaman shaida wajen gurganar da kaninsa a gaban Kotu.

Hauwa ta rasu ta bar yara biyu har da Jaririya yar wata tara.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN