Wata fitacciyar mata ta fasa gilashin Jirgin sama jim kadan bayan ya tashi yana tafiya cikin sararin samaniya saboda matsalar rushewar soyayya tsakaninta da masoyinta.
Malama Li mai shekara 29, ta tilasta matuki Jirgin Jaragen sama na Loong 8528 yin saukar bazata a filin saukar Jiragen sama na kasa da kasa a Zhengzhou Xinzheng da ke gundumar tsakiyar kasar China watau Sin.
Ma'aikatan filin saukan Jiragen sun ce Malama Li, ta kasa yin hakuri, ta yi ta kuka tare da bijirewa, har ta fasa gilashin Jirgin sama da take ciki, yayin da yake tafiya a sararin samaniya.
Sai dai bayanai sun ce Li ta kwankwadi kwalabe biyu na Lita 250 na barasa wanda ake kira "Baijiu" da ke dauke da kashi 35 zuwa 60 na barasa kafin ta shiga Jirgin.
Jirgin dai ya taso ne daga Xining babban birnin Quinghai da ke arewacin China, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Yancheng a gundumar Jiangsu na gabas.
Rahotun Isyaku Garba Zuru.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari