An sa tukwicin N5,000,000 don kamo madugun ‘yan bindigar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi alkawarin ba da tukwicin Naira miliyan biyar ga duk wanda ya ba da bayani a kan yadda za’a kama Adamu Aliero ko kuma ya kawo shi ko a raye ko a mace.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina CP Sanusi Buba ya ce Adamu Aliero shi ne jagoran wadanda suka kai hari a garin Kadisau na Karamar Hukumar Faskari ta Jihar, harin da ya yi sanadiyyar kashe sama da mutum 20.

CP Sanusi Buba ya ce bayanai sun nuna Aliero ya kitsa kai harin ne saboda ‘yan sanda suna rike da dansa mai suna Suleiman.
Don haka rundunar ke neman al’umma da su taimaka da bayanan da za su kai ga kama wanda ake zargin, za kuma a ba da ladan Naira miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka aka kai ga nasara.
A ‘yan kwanakin nan jihar Katsina ta yi fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda suka yi sanadin salwantar rayuka da dama.

https://aminiya.dailytrust.com.ng/an-sa-tikwicin-n5000000-don-kamo-madugun-yan-bindigan-katsina/

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari