Jama'a na tafka asarar gininsu bayan zargin soji sun yi rusau a Badariya Birnin kebbi

J
ama'a a garin Birnin kebbi na ci gaba da tafka asara a unguwar Badariya sakamakon rusau na gine ginensu da ake zargin jami'an soji daga Barikin soji na Barikin Dukku da ke Birnin kebbi ke aikatawa.

Wannan lamari ya dade yana haifar da yan kallo, a gefe daya kuma, bayin Allah na ci gaba da yin asara,  bayan an rushe masu gini.

Wani dadadden bayani shine cewa soji na da'awan cewa wannan yanki ya shigo cikin filin soji ne, sakamkon haka majiyar mu ta ce soji na kokarin kiyaye iyakokinta ne, sakamakon barazanar kutse da wasu mutane ke yi ta hanyar yin gini a filin soja ba tare da izini kon dalili ba.

Sai da mun gano cewa lamarin jayayya dangane dafilin ya kai gaban Kotu.

A gefe daya kuwa, wani mazauni unguwar Badariya da baya son a ambato sunansa ya shaida mana cewa " Abin da soji a Badariya ke aikatawa ya zarce ka'ida, idan ka je Sokoto soji basu da irin wannan katafaren fili a Kwannawa duk da yake Barikin Sokoto ya zarce na Birnin kebbi a yawa da fadi saboda Brigade ne na soji gaba daya."

"Haka zalika idan ka duba Rundunar soji na daya da ke Kaduna 1 Div, za ka fahimci irin girman wannan Bariki, amma basu ware irin wannan katafaren fili ba, to mi ya sa sai a gari kamar Birnin kebbi soji za su sami irin wannan katafaren fili.?"

" Idan ka duba daga katangar Bariki har zuwa ketaren tagwayen titi da ya ratsa yamma maso kudancin unguwar Badariya, har zuwa saman wajen da aka wargaza dutsen hanyar kauyen Kola, soji na da'awan cewa wannan katafaren fili nasu ne"

SHARHI

Sakamakon irin yadda wannan rikicin fili ya ki ci ya ki karewa tsakanin jama'a da soji  a  Badariya, Mujallar ISYAKU.COM na ba Gwamnatin jihar Kebbi shawarar  cewa lokaci ya yi da za ta sake duba tsarin yarjejeniyar ko dokar bayar da fili da ta yi ga soji a Badariya.

Ba daidai bane Gwamnati ta yi kasa a guiwa ta hanyar rashin tabuka komai dangane da rusau da ake zargin soji na yi na gidaje a Badariya bisa zargin kutse ga filinsu

Da farko dai Gwamnatyin jihar Kebbi ko ta zabi tsarin janye wannan yarjejeniya ko tsarin da aka bi wajen  bayar da filin ko ta rage girmansa saboda al'ummanta su sami sakewa da kwanciyar hankali, kamar yadda ake zaune lafiya tsakanin jama'a da soji a Barikin soji da ke Kwannawa a jihar Sokoto, Zuru, da babban runduna ta 1 na sojin Najeriya a garin Kaduna.

Haka zalika Gwamnati ta ba soji  kayyadadden lokaci domin su kewaye iyakan filinsu da gini, saboda kauce wa abin da suke kira kutse da ake yi wa filinsu.

Mun fahimci cewa rashin daukar ingantaccen mataki dangane da wannan lamarin zai iya taba martabar mahukunta a jihar Kebbi a fuskan talakawa, musamman wadanda aikin rusau ya tabasu kai tsaye.

Isyaku Garba Zuru

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN