Bayan kimanin mako daya da karewa cugar Korona a jihar Kebbi, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samun bullar cutar a jihar Kebbi.
A jihar Sokoto kuwa, kwanaki biyu kacal bayan sanar da karewar cutar, an samu karin mutane 12 sabbin kamuwa da cutar. Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana a yau 6 ga watan Yunin 2020, an samu sabbin masu cutar korona 389 a Najeriya.
A jihar Legas an samu karin mutum 66 da ke dauke da muguwar cutar, yayin da babban birnin tarayya na Abuja ke biye da sabbin mutum 50. A jihar Sokoto, an samu sabbin bulla goma sha daya (11) yayinda aka samu sabbin bulla biyu (2) a jihar Kebbi.
Ma'aikatar lafiyar jihar Sokoto ta bayyana cewa Almajiran da aka kawo daga jihar Kadina 33 da aka samu sabbin masu cutar a jihar. Jawabin yace, "Kwamitin yakar cutar COVID-19 ta karbi Almajirai 33 da aka kawo daga Zaria jihar Kaduna ranar 4 ga Yuni, 2020."
"Dukkan Almajiran 33 na killace a sansanin NYSC dake Wamakko kuma yayinda suka isa jihar muka dauki samfurinsu." "Amma kash! 11 cikin wadannan 33 sun kamu da cutar."
Rahotun Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari