Wata baiwar Allah mai matsakaicin shekaru ta jawo yan kallo bayan ta yanke jiki ta fadi kuma ta fara aman jini a kan Gadar Banex da ke Abuja babban birnin tarayya ranar Juma'a.
Rahotanni sun ce da farko matar bata nuna alamun wani rashin lafiya ba.
Saidai Sahara Reporters ta labarta cewa matar ta yanke jiki ta fadi, sakamakon haka aka sami rudanin tsakanin jama'a da ke wannan wurin a lokacin da abin ya faru.
Hakazalika an lura cewa jama'a sun tsorata, wasu kuma suna kyamar zuwa kusa da matar bayan ta fadi kuma ta suma jini na ci gaba da fitowa daga bakinta.
Daga bisani yansanda sun iso wajen suka dauke ta suka tafi da ita zuwa Asibiti domin samun kulawa.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari