• Labaran yau


    Wata daya da fara aikin dansanda, Amina Yusuf na cikin wadanda aka kashe a Isanlu

    Ranar Alhamis 5 ga watan Yuni wasu yan fashi da makami sun kai mumunan hari a garin Isanlu a karamar hukumar Yagba ta gabas suka yi fashi a bankin First Bank bayan sun kashe DPO tare da yansanda 7 a ofishin yansanda na garin.

    Daga cikin wadanda aka kashe har da wata yarsanda mai suna Amina Yusuf mai shekara 21 da ta kammala samun horon zama yarsanda wata daya da ta gabata kuma aka turota garin Isanlu domin fara aiki.

    Rahotanni sun ce yan fashin sun kai harin ne da karfe 4:30 na yamma kuma sun shafe fiye da awa daya suna fashi a garin.

    Wannan ya biyo bayan tura jami'an tsaron soji da yansanda masu yawa zuwa Kabba domin tabbatar da dokar hana zirga zirga sakamakon matsalar cutar Korona.

    DAGA ISYAKU.COM
    Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
    https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

    Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
    LATSA NAN

    SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

    Facebook.com/isyakulabari

    Twitter.com/isyakulabari
    • Facebook Comments
    Item Reviewed: Wata daya da fara aikin dansanda, Amina Yusuf na cikin wadanda aka kashe a Isanlu Rating: 5 Reviewed By: -
    Koma Sama