• Labaran yau


  Hotuna: An kashe dalibar Jami'a mai dauke da juna biyu tsawon wata 7

  An sami gawar wata daliba wacce ke karatu mataki na Digiri na biyu mai suna Shomuyiwa Azeeza wacce ke dauke da juna biyu tsawon wata 7 a dakinta a Jami'ar jihar Oyo da ke birnin Ibadan.

  Bayanai sun ce an ga alamar cewa an yi amfani da katon dutse ne aka doke ta a kai.

  Sai dai wata sanarwa da hukumar Jami'ar ta fitar ya musanta cewa an yi wa dalibar fyade ne har ta mutu kamar yadda labari ya watsu a shafukan sada zumunta.

  Hakazalika bayanai sun tabbatar cewa Kwamishinan yansandan jihar Oyo ya je har dakin dalibar kuma tuni yansanda suka fara gudanar da bincike kan musabbabin dalibar.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna: An kashe dalibar Jami'a mai dauke da juna biyu tsawon wata 7 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama